Zamu Saki Sambo Dasuki Bisa Sharadi Guda –  BUHARI


Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Shugaba Muhammad Buhari ya bayar da umarnin Sakin Tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin tsaro, Sambo Dasuki idan har ya mayar da kudaden da aka sace ta hannunsa.
Da yake tabbatar da haka, daya daga cikin makusanta Shugaban kasa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya nuna cewa Buhari da kansa ya nemi Jin dalilin da ya sa ake ci gaba da tsare Dasuki inda aka nuna masa akwai tuhumomi guda uku a kansa.
A cewar majiyar Shugaba Buhari ya nemi a gaggauta bin matakan kwato wadannan kudade ta yadda za a samu hujjar Sakin Dasuki. Wannan bayanin ya yi daidai da wanda aka wallafa a cikin sabon littafin nan na tarihin Buhari wanda Farfesa John Paden ya rubuta kwanan nan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like