Zan binciki Buhari idan aka zabe ni shugaban kasa – Atiku


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma mai neman jam’iyar PDP ta tsayar da shi takara a zaben shekarar 2019 ya ce zai binciki batun cinikin makamai da gwamnati mai ci a yanzu take saya.

Da yake magana a wata tattaunawa da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, Atiku ya ce an dauki lokaci mai tsawo ba tare da kawo karshen rikicin Boko Haram ba.

“Bayan shekara takwas, har yanzu gwamnatin Najeriya na yaki da kungiyar Boko Haram da basu da wani cikakken horo na musamman,”yace.

“Ina so na zama shugaban kasar Najeriya, saboda zan gudanar da wasu abubuwa da na kasa yi lokacin ina mukamin mataimakin shugaban kasa, zan binciki yadda gwamnati ta kasa kawo karshen Boko Haram tsawon shekaru zan kuma binciki batun sayan makamai da wannan gwamnati ta sayo.”

Ya kuma ci alwashin yaki da cin hanci da rashawa inda ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da kare wasu mutane wadanda kamata ya yi su fuskanci shari’a.

You may also like