Rikici tsakanin tsohon Gwamna Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fara kai wa matukar tafarfasa.
A sanarwar da Kwamishinan yada labarai Malam Muhammadu Garba ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa matukar ‘yan Kwankwasiyya suka ci gaba da yada karya akan Ganduje to kuwa zai cire jar hula ya bankado bayanai ya mikawa EFCC domin bincikar Kwankwaso.