Gwamna ABDULLAHI UMAR GANDUJE na Jihar Kano a wannan tattaunawar da ya yi da manema labarai a Sakkwato ya yi bayanin wadanda ke ruruta wutar rikici a Gwamnatinsa da matakin da suka dauka na taka masu burki. Gwamnan wanda tuni dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Magajinsa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fito fili ya bayyana cewar ya shirya tsaf domin bayyanawa duniya ko wane ne Kwankwaso.
Ganduje wanda shine kan gaba wajen ribantar akidar Kwankwasiya bai yi kasa a guiwa ba wajen bayyana cewar ayyukan da Kwankwaso ya gudanar a mulkinsa ayyuka ne na yaudara da sauran batutuwan da ya bayyana a wannan tattaunawar wadda SHARFADDEEN SIDI UMAR ya nado mana kamar haka:
Mene ne dalilin shirya wannan taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC Kano a Sakkwato?
Mun shirya wannan taron ne domin mu kawo gyara kan yadda ake tafiyar da jam’iyya daga tafiya dogon hutu bayan kafa Gwamnati zuwa ci-gaba da gudanar da ayyukan jam’iyya bayan samun nasara, domin bai kamata jam’iyya ta zama da an shiga mulki shi kenan an manta da ita ba. Muna son jam’iyya ta zama tana da rai a koda yaushe. Daga cikin ayyukan jam’iyyar siyasa shi ne ta rika karbar korafe-korafe da matsalolin al’umma da bukatocinsu ciki har da nazarin ayyukan jam’iyyun adawa. Mun aminta za mu rika gudanar da taron jam’iyya a matakin mazaba a kowane wata ta yadda abin da aka tattauna a mazaba za a mika rahoto a matakin Karamar Hukuma wadanda su ma za su tattauna a kowane wata daga nan su kuma sai su mika rahoto ga jam’iyya a matakin jiha domin dubawa da daukar matakin da ya kamata. Matsalolin jam’iyya, kura- kuran da aka samu, hanyoyin samun gyara da tsare-tsaren jam’iyya a Kundin Tsarin Mulkin da sauransu shine abin da ya kawo mu Sakkwato domin mu tattauna wadannan batutuwan da abin da ya shafi tsayar da ‘yan takara nagari domin kaiwa ga gaci.
Mun kuma zabi Sakkwato ne saboda tarihin da take da shi na shugabanci nagari tun daga zamanin Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo zuwa yau. Domin wannan taron mun zo tare da dukkanin shugabannin jam’iyya tun daga matakin karamar hukuma zuwa jiha da dukkanin shugabannin kananan hukumomi 44 da ‘Yan Majalisar Jiha da na Tarayya da ‘Yan Majalisar Zartaswar Jiha da shugabannin jam’iyya a matakin kasa a karkashin jagorancin Shugaban APC na Kasa, Cif John Oyegun baya ga dattawan siyasar Kano da suka albarkaci wannan taron na karawa juna sani na kwanaki uku.
Taron ya zo a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cikin mawuyacin hali tare da neman masu rike da madafun iko su share masu hawaye. Ko me za ka ce a kai?
Shakka babu al’ummar Nijeriya na da kyakkyawan zato ga mulkin APC, ba shakka an fito kwai da kwarkwata an zabi APC. Kamar yadda a ka sani APC ta dauki alkawura guda uku gabanin zabe. An ga yadda ake kaiwa Malamai da al’ummar gari hare-hare da su kansu coci- coci duk ba a tsira ba, kisan gilla a fili ake yi kowa bai tsira ba. Buhari ya zo ya ce zai yi maganin wannan ibtila’in, abin tambaya shin maganin wannan matsalar an same shi ko ba a same shi ba? A inda aka fito Kananan Hukumomi a Borno suna hannun Boko-Haram amma yanzu babu Karamar Hukuma ko daya hannun mayakan, a yau babu inda ake sa injin din yankan katako a na fille kawunan jama’a. Watakila an yi yakin ne domin a raba Nijeriya ko kuma ba a ayi yakin da zuciya daya ba, hatta makaman da sojojin ke amfani ba na kwarai ba ne, za ka ga soja na harbi amma bindiga na zafi. Idan da yau Buhari bai hau mulki ba shin ‘yan Arewa a wane hali muke?
Baya ga wannan ya ce zai yi maganin barayin Gwamnati, zai yaki cin hanci da rashawa. Shin Buhari macuci ne marar gaskiya? Wai shin ba da ganinsa tamkar ga gaskiya nan ta na tafiya da kafafun ta ba? Shin Buhari bai kama wadanda ake ganin ba su kamuwa ba? Anya bai kama wadanda ke kama mutane ba? Haka ma duk dan Nijeriya ya san darajar fetur ta karye bakidaya kuma babu wani siddabarun da za a yi idan ya karye illa a komawa gaskiya. A da ana hako mai sosai amma yanzu tun da dan Arewa ne ke mulki sai a ka rika yi masa zagon kasa. Muhammadu Buhari ya kuma ce a daina shigo da shinkafa domin hana shigowar zai sa mu koma gona saboda abinci ya wadata. Ina buga kirjin cewar jam’iyyar APC ta na cimma burin da aka zabe ta. Lallai Buhari ya na kokari kuma tattalin arzikin kasa zai dawo, lamurra za su daidaita da yardar Allah.
Bisa ga yadda al’amurra suka kasance a Kano da yadda Gwamnoni ke binciken wadanda suka gabace su ko akwai batun binciken Gwamnatin da ta gabata?
Lallai ne jihohi da dama a na gudanar da bincike domin yaki da cin hanci da rashawa. Amma dai babu wani dalilin da zai sa in gudanar da bincike kan Gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso da ta gabata. Gwamnatina ta himmatu ne wajen sauke nauyin da al’umma suka dora mana. Don haka ba batun binciken Magaji na ne a gabana ba.
Matsaloli sun yi kamari tsakaninka da Kwankwaso. Jama’a za su so sanin ainihin tushen wannan matsalar?
Ka je Jihar Gombe ka tambayi Gwamna Dankwambo me ya faru tsakanin a da Magajinsa Danjuma Goje. Ba zan so yin bayanin abubuwan da suka faru a yanzu ba, domin yanzu haka ina rubuta littafi kan wannan hayagagar kuma ba na son in ragewa littafin armashi tun a yanzu. Har na kammala zan fitar da littafin amma sai na ga akwai bukatar kara wani babi daya mai matukar muhimmanci. Sunan littafin Zama Mataimakin Gwamna A Nijeriya: Matsaloli Tsakanin Gwamnan Da Ya Bar Gadon Mulki Da Magajinsa. Idan na fitar da littafin jama’a za su ga duk wata rikita-rikitar siyasa dake faruwa tsakanin Gwamna da Mataimakinsa. Amma a yanzu da kuke son in fede biri har wutsiya, to ba zan fede ba.
Kano babbar cibiya ce ta kasuwanci. Za mu so sanin harajin dake shigowa asusun Gwamnati a kowane wata?
Karbar haraji a hannun talaka a irin wannan lokacin abu ne mai wahala. Duk da haka muna iyakar kokarinmu, jama’a na bayarwa saboda sun gamsu da aikin da ake yi masu. A yanzu harajin mu ya tashi daga naira milyan 600 zuwa bilyan uku a duk wata, zuwa nan gaba fatar mu ita ce harajin ya kai naira bilyan 10 a kowane wata. Dukkanin kudaden da aka samu na haraji a na gudanar da manyan ayyuka ne da su domin jama’a su gani a zahiri abin da ake yi da kudaden su.
Ko wadanne irin kalubalen gudanar da mulki kake fuskanta?
Bukatu sun yi yawa, matsalolin da ake son magancewa suna da yawa, ga su nan a fannin ilimi, kiyon lafiya, samar da ruwan sha da inganta tsaro da sauransu. Duk da haka muna kokari kwarai domin ganin mun sauke hakkin jama’a dake kan mu.
Ko mene ne Ganduje ke yi a Kano wanda ya bambanta da yadda abubuwa ke gudana a baya?
A yau ko makaho ya san ana aiki a Kano. Manya- manyan ayyukan da a ka fara wadanda ba a kammala ba, yanzu muna nan muna kokarin kammala su. Aikin dam din Chalawa wanda aka fara aka watsar yanzu mun yi nisa wanda bayan kammala shi za mu samu wutar lantarki ta Jiha. Ga gadar Sabon Gari a na nan ana yi da sauran kananan ayyuka duka muna nan muna karasawa baya ga sababbin ayyuka da muka bullo da su. Aikin hanyar wucewa ta kasa muna nan muna yi, masu zuwa Kano daga Katsina da ke awa daya cik a tsaye yanzu za su rika wucewa sululu su shigo gari. Ku tambayi manoma shin ba mu ba su naira milyan dari na iri ba? Abin da zan bayyana a nan shine ci-gaba irin na shafa hoda wato ci gaba irin na yaudara ya zo karshe a Kano.
Ba za ka rasa abin cewa kan rikita-rikitar Shugabancin Jam’iyyar APC A Kano ba?
Insha Allah karshen wannan matsalar ta zo. Dama can mutane biyu sune matsalar wato Shugaban Jam’iyya da Sakataren Tsare-tsare wadanda sune ke yin zagon kasa ga Gwamnatin Kano. Shugabannin jam’iyya sun cimma matsayar korar su, su kansu masu shata dokoki duka sun sanya hannun amincewa da korar su ta yadda mutane sama da 300 suka sanya hannun amincewa. Ita kanta uwar jam’iyya ta kasa sun zo sun binciki yadda matsalar take, kuma za su bayyana matsayar su, amma dai bayanin da muka samu shine su kansu sun aminta da matakin da muka dauka. Abin da nake son a gane shine rigima a siyasa ba bakon abu ba ne, hayaniya a siyasa ita kanta siyasa ce.