
Asalin hoton, Aminu Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan ayarin motocinsa a Sokoto tare da shan alwashin gurfanar da waɗanda suka kai harin a gaban kotu.
A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai Muhammad Bello ya fitar, wasu waɗanda ake kyautata zaton zauna garin banza ne suka yi ruwan duwatsu ga ayarin motocin gwamnan a cikin birnin Sokoto a lokacin da yake komawa birnin daga yaƙin neman zaɓen da yaje Ƙananan Hukumomin Wamakko da kuma Silame.
Cikin waɗanda suke cikin tawagar gwamnan a lokacin da aka kai harin har da ɗan takarar gwamna na PDP a Sokoto wato Mallam Saidu Umar da Janar Aminu Bande da mataimakin gwamnan Sokoto Honorabul Sagir Bafarawa, kuma dukansu babu wanda ya ji rauni kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sai dai sanarwar ta ce akwai motoci biyu waɗanda aka lalata a lokacin harin.
A yayin wata hira da ƴan jarida, gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin waɗanda suka kai harin kuma za a kai su kotu.
A wata hira ta daban da kwamishinan watsa labarai na jihar Honorabul Akibu Dalhatu ya yi da manema labarai, wanda ake zargi shi ne jagoran maharan wato wani Abu Mai Adda na daga cikin waɗanda hukumar tsaro ta farin kaya wato NSCDC ke nema ruwa a jallo kuma tuni aka kama shi.
Kwamishinan ya kuma ce ana zargin Mai Adda da lalata wasu motocin ayarin gwamnan da kuma sace babura biyar bayan kai hari ga magiya bayan PDP a lokacin yaƙin neman zaɓe a Wamakko.