Zan iya komawa yakin neman zabe jihar Benue- Buhari


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ce watakila zai iya komawa yakin neman zabe jihar Benue kafin  zaben shakerar 2019.

Ya bayyana haka a Makurdi lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar a ziyarar da  ya kai.

Buhari wanda yaje jihar a cigaba da ziyarar da yake ya zuwa jihohin da suka fuskanci rikici har ta kai ga asarar rayuka masu yawa.Shugaban yana mai da martani ne kan jerin bukatun da mahukunta a jihar suka mika masa.

“Idan na dawo yakin neman zabe, zan iya yin alkawari,” Femi Adesina mai magana da yawun shugaban ƙasar ya jiwo shi yana fada.

Ya nemi mutanen jihar Benue da su yi addu’a a samu habakar tattalin arziki inda ya ce ba zai yi wani alkawari ba a yayin ziyarar.

You may also like