Zan Kawo Ƙarshen Yunwa Da Talauci A Najeriya Nan Da Shekara Ta 2025 Idan Buhari Ya Bani Izini –Obasanjo


obasanjo

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya shawarci jihohi da kuma gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake jagoranta da su haɗa hannu da manoma a yunƙurin kawar da yunwa kafin shekara ta 2025.

Obasanjo yayi wannan kiran ne a gidansa dake Abeokuta babban birnin jihar Ogun, lokacin da ƴan ƙungiyar haɗakar manoma ta Egba suka kai masa ziyarar ban girma.

Obasanjo ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban wata ƙungiya da ake kira ‘Zero Hunger Farmers Organisation in Nigeria’ a turance yace sun ƙudiri aniyar kawar da yunwa ta hanyar ƙara samar da abinci ta yadda zai zamanto babu wani ɗan Najeriya da zai kwanta da yunwa.

Yace idan da za a basu goyon baya da kuma ƙarfafa musu gwiwa manoma zasu samar da abinci wadatacce kuma mai sauƙin farashi, wanda hakan zai haifar da wadatar abinci a cikin ƙasa.

A tabakin Obasanjo “gwamnati zata iya taimakon manoman dake ƙasarnan ta hanyar tsare-tsare da kuma samar da yanayi mai kyau da zai haifar da samar da abinci”.

Tsohon shugaban ƙasar ya shwarci manoman da sufara haɗakar noman:Kifi,kaji,rogo da kuma shinkafa kafin su shiga noman samar da ƴaƴan itatuwa wanda yace hakan yana ɗaukan lokaci kafin afara cin amfaninsu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like