‘Zan koma fim idan na yi ritaya’- Joshua



Joshua

Asalin hoton, OTHER

Dan wasan damben Burtaniya, Anthony Joshua ya ce zai koma fitowa a tauraron fina-finan Hollywood idan ya yi ritaya daga dambe.

Joshua wanda ya taba lashe kambun duniya har sau biyu, ya fada wa mujallar GQ ta Amurka cewa wasan dambe ya bude mashi hanyoyi da suka sa ya fara tunanin gwada wasan kwaikwayo.

”Ina so in gwada wani abu bayan dambe da nafi kwarewa a kansa,” a cewar Joshua.

Ya kara da cewa ” Ina ganin bayan dambe zan koma fitowa a fina-finai saboda na yi talloli na ga yadda ake shirya su, kuma ba ni da matsala a gaban kyamara.”



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like