Zan tsaya takarar shugaban kasa idan Buhari ba zai tsaya ba -Yerima


Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima,  ya ce zai yi takarar shugaban kasa a shekarar 2019 idan har shugaban kasa Buhari yaƙi yarda ya nemi takara a karo na biyu.

Ya fadawa manema labarai jiya Lahadi a Abuja, ya ce sanarwa ba za ta kawo tazgaro ba ga goyon bayansa ga shugaba Buhari idan ya yanke shawarar sake tsayawa takara a shekarar 2019.

Yerima da ke wakiltar mazabar Yammacin Zamfara a majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar APC, shine ya goyi bayan kudirin da aka gabatar a taron kwamitin  zartarwar jam’iyar APC, na neman Buhari ya sake tsayawa takara a 2019.

Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai yi takara da Buhari ba amma ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa babu wanda zai yi allawadai dashi idan yanke shawarar tsayawa takara matuƙar Buhari yaki amincewa da tsayawa takara.

You may also like