Ayodele Fayose gwamnan jihar Ekiti yace bayan ya yi ritaya daga siyasa zai zama fasto a majami’a.
Ya ce abinda yake da burin yi bayan ya kammala mulkinsa na gwamnan jihar shine ya zama shugaban ƙasa daga nan kuma zai koma cikakken limamin coci.
Fayose yace farin jininsa da kuma ikon faɗa aji da yake da shi za su taimaka masa wajen cimma burinsa.
Ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin manema labarai a Lagos.
“Babu wani mutum da mai hankali da zai ce bai san waye Ayo Fayose ba kuma matakina na zama shugaban kasa a zuci yake ta wani bangaren kuma a fili saboda idan lokacin ka yayi zai nuna,” yace.
“Ni wani mutum ne mai muhimmanci da Allah ya halitta a wannan lokaci zan zama limamin coci tare da wata babbar coci.
“Bayan na zama shugaban ƙasa Najeriya zan zama limamin coci mai ƙarfin faɗa aji a duk fadin duniya.”
Fayose yayi kaurin suna wajen sukar manufofin shugaban kasa Muhammad Buhari.