Zance Na Ilimi Daga Masu Shi: Sauraro Da Alfanunsa – Malam Nabil Bello Sa’id


nabil-bello

 

Wani daga cikin magabata na k’warai ya yi wa d’ansa nasiha, ya ce: “Ya kai d’ana ka koyi kyakkawan sauraro kamar yadda ka ke koyon kyakkyawan zance.” Wannan batu yana da matukar muhimmanci amma ga wanda ya yi tunani mai zurfi. Yawanci cacar baki da fad’ace-fad’ace suna aukuwa ne saboda matsalar sauraro.

 

Bari ka gani in maka dalla-dalla. Masana halin dan Adam sun kasa mutane zuwa gida hudu wajan sauraro:

 

1. Akwai wanda idan kana magana hankalinsa yana wani waje, saboda haka sai ya fahimci magana rabi-da-rabi. Misali, wannan yana faruwa a yajan karatu.

 

Tare za ku je karatu da abokinka, ku zauna waje guda, ka ji an tashi ana rantse -ranste wannan ya ce Malam ya ce idan za a wanke kafa sai an had’a da idon sawu, wannan ya ce cewa ya yi zuwa idan sawu amma ban da idon sawun.

 

Idan kuma ka bibiya duka ya fad’a, amma hankalin wancan yana wani guri sanda aka fadi ra’ayin farko, wancan kuma hankalinsa yana wani guri aka fadi na biyu.

 

2. Wani kuma daga ka fara magana sai ya rik’a neman ya ji ka fad’i wani abu a cikin zancenka, saboda haka daga ya ji ka fad’i abin sai ya rik’e shi caraf ya kuma manta da sauran.

 

Me yiwuwa ma kai ba shi ne ra’ayinka ba, watak’ila labarin wani kake bayarwa amma saboda yana jiran ka fadi abin, daga ya ji ka fad’a sai ya manta da duk sauran labarin. Idan kana so ka gane wannan sosai, ka lura da yadda d’an siyasa musamman irin na k’asarmu suke sauraron abokin adawarsa na siyasa, jira suke kawai su ji kuskure sai ka ga sun ta da hankalin duniya, don bukatarsu ta biya.

 

3. Shi kuma wannan idan kana magana sai ya rika tunanin a cikin abin da kake gaya masa ina ne ya shafe shi. Bai damu da labarinka ba saboda bai ba shi muhimmanci ba. Muhimmancin labarinka shi ne ina ne ya shafe, ko me zai kawo masa maslaha. Wannan kuskuren ina ga ya fi kowane yawa a cikinmu. Mai irin wannan sauraron jira yake ka kai wata gaba sai ya katse ka, shi ma sai ya gaya maka nashi labarin.

 

Wannan ba zai zama laifi ba idan ka ba shi cikakkiyar dama ya gama yi maka bayani. Amma sau da yawa za ka kai wa wani kuka, maimakon ya share maka hawaye sai ya shiga gaya maka ai shi ma ga nashi labarin. Shi ma fa haka yake ji. Mun fi yin irin wannan kuskuren idan mun je duba mara lafiya.

 

Shi mara lafiya so yake ya ga an tausaya masa. An gane yadda yake ji duk da ba za a iya cire masa cutar ba. Idan ka je duba mara lafiya kar ka ka damu da ba shi labari ai kai ma ka taba yin irin wannan cutar ka shiga ba da tarihi. Idan har za ka yi masa labarinka ya zama a matsayin misali.

 

Kamar idan za ka ba shi shawarar wani magani da ka sani, sai ka ce ai ni ma na taba yin wannan cutar amma da na sha magani kaza ya yi min amfani sosai.

 

4. Wani kuma idan ka fara magana zai natsu ya saurare ka tun farko har karshe ba tare da katse ka ba, kuma zai alak’anta maganarka ta farko da ta k’arshe. Wannan shi ne irin sauraro da ake nema, kuma irinsa ne yake amfani, kuma shi ne ke kawo zaman lafiya.

 

Sauraro don ka k’aru, ba don ka k’arar ba. Yi k’ok’ari ka gane abin da ake gaya maka sosai domin shi ne mataki na farko ida kana so a gane ka. Wannan dai tunatarwa ce gare ni kafin ku. Da fatan kun yi kyakkawan karatu, don samun kyakkyawar fahimta. Allah ya gyara d’abi’unmu, ya sa mu zauna lafiya da ‘yan uwanmu gaba daya. Sai kun sake ji na.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like