Dubban ‘yan kasar Siriya da ke zama a kasashe daban-daban suka yi zanga-zanga domin yin Allah wadai da yanayin yaki wanda ke kara ritsawa da fararen hula

Daya daga cikin Siriyawa da suka yi zanga-zangar a kasar Turkiyya cewa ya yi. “Birnin Aleppo ya dade da fiskantar ta’addanci. Musamman yanzu da wadannan ‘yan ta’adda da ake kira IS. Muna cikin mayuwacin hali bisa bala’o’i biyu da suke fiskanta mu, ga ‘yan ta’adda gefe daya, gefe na biyu kuma ga farmakin jiragen sama. Babban abin da ya kawo rudani shi ne man’yan kasashe da suka fi karfi a duniya Rasha da Amirka wadanda suke neman karfin iko da birnin na Aleppo. Don haka talakawa suna cikin tashin hankali.