Yau wasu kungiyoyin fararen hula a Najeriya ke gudanar da zanga zanga a birnin Abuja, dan nuna bacin ran su da yadda wasu hukumomin gwamnatin kasar ke dibar ma’aikata a boye.
Masu zanga zangar na bukatar ganin shugaban kasar ya gudanar da bincike dan hukunta jami’an da suka dibi ma’aikatan ta hanyar da basu kamata ba, inda suke cewa akasarin wadanda aka dauka yan uwan yan siyasa ne da masu rike da mukaman gwamnati.
Dr Emman Shehu daya daga cikin masu shirya zanga zangar ya bayyana yadda ma’aikatu da Hukumomin gwamnati ke coge wajen diban ma’aikata aiki.
Dr.Emman ya ce, hakan ya sabawa canji da suka zaba, da kuma yakin da gwamnatin kasar keyi na kakkabe cin hanci da Rashawa.