Zanga-zangar dalibai a Afirka ta Kudu


 

 

‘Yan sanda a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu sun yi amfani da hayaki mai sa kwala domin tarwatsa wasu dalibai da ke yin zanga-zanga.

 

Daliban sun yin zanga-zangar ne a kan bukatar ganin gwamnatin ta samar da illimi ga kowa kana kuma kyauta.Wani gidan talabijin na Afirka ta kudu ANN7 ya nuna hotunan ‘yan sanda da dalibai da dama wadanda suka jikkata.Yau makonnin biyu ke nan da daliban a Afirka ta Kudu ke yin zanga-zanga  bayan da gwamnatin ta amince da karin kishi takwas cikin dari na kudaden makaranta.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like