Zanga-zangar kyama ga Mugabe a Zimbabuwe


Wani taron kallon wasan kwallon gora ko Criket da aka gudanar a wannan Asabar a Bulawayo ya rikide zuwa zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin Shugaba Robert Mugabe.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa a tsakiyar wasan ne ‘yan kallon suka mike tsaye suna kada tuta da rera taken kasar tasu. Wasu daga cikin masu zanga-zangar na dauke da kwalaye masu dauke da kalaman nuna kosawarsu da mulkin Shugaba Mugabe musamman kan matsalar tattalin arzikin da kasar take fama da ita da ‘yan kasar ke dangatawa da kasawar mulkin shekaru 36 na gwamnatin Shugaba Mugabe.

Dama dai tun da sanyin safiyar wannan Asabar jami’an ‘yan sanda su kame wasu mata kimanin 10 mambobin Kungiyar WOZA wata kungiyar mata masu da’awar ceto kasar Zimbabuwe wadanda suka gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa da mulkin Shugaba Mugabe a bakin kofar filin wasan na birnin na Bulawayo.

You may also like