Zanyi Aiki da PDP dan kawo karshen rikicinta-Jonathan


Zanyi aiki da da PDP Dan kawo karshen rikicin Jam’iyyar inji tsohon shugaban kasa Goodluck ebele Jonathan.

Tsohon shugaban kasa Goodluck ebele Jonathan yace zai cigaba da aiki da sassan kungiyar PDP Dan kawo karshen rikicin Jam’iyyar ta PDP.

Jonathan yace magoya bayan jam’iyyar dasu daina amfani da jita-jitar kafafen watsa labarai.

A maganar da maibawa tsohon shugaban kasa shawara ikechukwu eze,yace tsohon shugaban kasa ya nuna jindadinsa yadda yaga jam’iyyar ta zama tsintsiya madaurinki,daya  ta yadda yaga kokarin magoya bayan jam’iyyar da shuwagabannin PDP din ke kokarin kawo karshen rigimar da ke jam’iyyarta PDP.

You may also like