An Zargi Rundunar Sojin Nijeriya da Tafka Karya


 

 

A ranar Talatar da ta gabata ne kakakin rundunar sojin Nijeriya Kanal Sani Usman Kukasheka ya sanar da cewa rundunar sojin Nijeria ta kwace garin Malam Fatori daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai wata majiya a rundunar sojin ta musanta wannan batu, ta bayyana cewa har yanzu garin Malam Fatori na hannun kungiyar ‘yan ta’addan. Jami’in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce babu gaskiya a ikirarin da rundunar ta yi cewa ta fatattaki mayakan Boko Haram daga garin.

Ya kara da cewa ‘yan Boko Haram din ne suka kora sojojin suka saka su suka janye a ranar Talatan, kuma an kashe wasu daga cikinsu, yayin da aka nemi wasu aka rasa.

Rahotanni daga yankin na nuna cewa har yanzu ana cigaba da gumurzu a tsakanin rundunar sojin gamayya ta kasashen da ke makwabtaka da tafkin Chadi da ‘yan kungiyar Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like