Zargin Cin Zarafin ‘Yan Gudun Hijira Boko Haram


4bkb5ee464cac0gphy_800c450

 

A wannan Litinin ce kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (HRW) ta zargi wasu jami’an gwamnatin Nigeria da yin lalata da ‘yan matan da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da yaudararsu don yin lalata da su.

kungiyar Ta kara da cewa ta samu bayanin yin lalata da kuma fyade kan mata da ‘yan mata 43 da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira bakwai da ke Maiduguri, a jihar Borno.

A rahoton HRW ta kuma zargi gwamnatin kasar da rashin yin abin da ya kamata wajen kare irin wadannan matan.

Wadanda zargin ya shafa sun hada da jami’an gwamnati, ‘yan sanda da kuma sojoji.

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda wadanan matan da ‘yan mata basu samu kula da suke bukata ba bayan bala’in da suka gani a rikicin boko haram, sai kuma gashi suka gamud a irin wannan ta’asar, wanda a cewar kungiyar abun kunya ne da takaici, duba da yadda wadamda ya kamata su kare wadanan matan sai ya kasance suke ke azabta masu ta hanyar cin mutuncinsu.

Wasu mata hudu da lamarin ya shafa sun shaidawa kungiyar cewa an basu kwayoyi suka sha, kafin daga bisani ayi masu fyade.

Sauren matan 37 sun shaida cewa ana kaisu suna lalata da jami’an ta hanyar yi masu alkawarin karya na aure ko kuma basu tallafin magunguna ko kuma kudi.

Sannan dayewa daga cikinsu sun ce anyi watsi dasu a lokacin da suka dauki ciki, lamarin da ya jefa su cikin mawuyacin hali dasu da ya yan nasu.

Biyo bayan wannan zargin dai shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa, domin daukar mataki.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Litinin, ta bayyana matukar damuwa ga rahoton na Human Rights Watch, tana mai kira ga ‘yan sanda, da gwamnonin yankunan da abun ya shafa, da su binciki wannan zargi ba tare da wani bata lokaci ba.

Mahukuntan Najeriya dai sun ce, suna daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na baiwa ‘yan gudun hijirar kariya, yayin da sojojin kasar ke ci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram a dukkanin sassan arewa maso gabashin kasar, a wani mataki na kokarin mai da ‘yan gudun hijirar zuwa garuruwan su na asali.

Jihar Borno dai na daga cikin yankunan Najeriya dasuka jima sun fuskanatar matsalar ‘yan ta’adda na Boko Haram, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane kimanin 20,000 tare da cilastawa wasu mutane milyan biyu da dari shida kauracewa gidajensu.

You may also like