Zargin Kayishema da kisan kare dangi | Labarai | DW



Mutumen nan da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen kisan kiyashin Rwanda a shekarar 1994, ya gurfana a wannan Jumma’ar a gaban kotu, a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Fulgence Kayishema, ya shiga hannun hukuma ne a makon jiya, bayan da ya shafe shekaru 20 yana kuli-kurciya da mahukunta da ke cewa ya yi ajalin fiye da mutane dubu biyu a wata majami’ar da ke yankin Nyange, na Arewa maso gabashin Rwanda.

Alkalan kotun na Majalisar Dinkin Duniya na tuhumarsa da zama silar kone majami’ar da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka.





Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like