Zargin rufe bakin ‘yan fafutika a Najeriya


A cewar rahoton da Kungiyar Amnesty ta fitar a ranar ta Laraba ta na da bayanai na jami’an tsaro sun tsare masu fafutikar Biafra, wasu sun bace baya ga wadanda suka rasu a hannun jami’an tsaro a Najeriya.

18380392_303

 

 

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa Najeriya na kokari da barazana ta rufe baki da ma yin barazana ga ‘yan jarida da masu zanga-zanga.

A cewar kungiyar wacce ke da ofishinta a birnin London cikin zanga-zangar da ta bayyana a baya-bayan nan akwai hana masu fafutika daga kungiyar nan mai kokari na ganin ansako ‘yan matan Chibok sama da 200 da ke hannun Boko Haram, da hana ‘yan Shi’a zanga-zangar a sako malaminsu bayan tsawon lokaci ya na hannun mahukunta da masu fafutikar samun ‘yancin yankin Biafra a Kudu maso Gabashin na Najeriya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like