Ministan Wutar Lantarki Ya Kunyata Yayin da Wuta ta Dauke Yana Kan Mambari


 

 

A jiya Talata ne a ka gudanar da wani taron bunkasa wutar lantarki a Nijeriya a otel din Eko da ke jahar Lagos mai taken ‘Power Nigeria’.

A dai-dai lokacin da ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje a Nijeriya Babatunde Fashola ya hau mambari domin ya fara jawabinsa, sai wutar lantarkin ta dauke, al’amarin da ya bashi matukar kunya.

Hakan ya sa ya bayarda jawabin nasa cikin duhu duhu. Faduwa ta zo dai dai da zama kenan.

Wani mutum mai suna Dolapo Oni shi ya yada a shafinsa na Twitter hotunan ministan a yayin da ya ke kokarin mazewa a cikin wannan al’amari

Da ga gefe guda kuma za’a iya cewa halin da Nijeriya ke ciki a bangaren wutar lantarkin ya kusa zuwa karshe a yayinda kasar zata gudanar da wani taro inda za ta tatttauna da kwararru 3000 daga kasar Amurka, Nahiyar Turai da Asiya akan matsalar wutar lantarkin da kuma mafita.

 

Taron ya samu goyon bayan makarantar koyar da ilimin wutar lantarki, hukumar bunkasa zuba jari a Nijeriya, gwamnatin Bayelsa, hukumar kula da wutar lantarki da sauransu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like