Zarif: Trump Ba Shi Da Hurumin Karya Yarjejeniyar Nukiya Da Aka Cimmawa Da Iran


4bmtd33ebd582clmn4_800C450

4bmtd33ebd582clmn4_800C450

Ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ba ya da hurumin karya yarjejeniyar Nukiliya da manyan kasashen duniya suka cimmawa tare da Iran.

Muhammad Jawad Zarif ya bayyana hakan ne a jiya  a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron tattalin arziki da ake gudanarwa a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ya ce furucin da Donald Trump ke yi kan yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran kalamai ne masu ban makaki.

Zarif ya kara da cewa idan har Trump ya dauki wannan mataki ba ya nufin kawo karshen duniya, kuma hakan zai mayar da shi saniyar ware hatta a cikin turawa masu kawance da Amurka.

A jiya ne dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da zama, inda ya jaddada cewa bisa dogaro da rahotannin hukumar nukiliya ta duniya kan shirin Iran na nukiliya, Iran ba ta saba wa ko daya daga cikin abubuwan da aka cimma yarjjeniya da ita ba.

You may also like