An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Wani Dan Nijeriya A Singapore


 

Rahotanni daga kasar Singapore sun jiyo mahukuntan kasar suna cewa an zatar da hukuncin kisa a kan wani dan Nijeriya da kuma dan kasar Malaysia saboda samunsu da aka yi da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Kafafen watsa labaran kasar Singapore din sun jiyo  hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasar, cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce an kashe Chijioke Stephen Obioha, dan Nijeriya, a gidan yarin Changi da ke kasar a safiyar yau  Juma’a tare da wani dan kasar Malaysia wanda shi ma aka same shi da laifin fataucin muggan kwayoyin.

A watan Aprilun 2007 ne aka kama Mr. Obioha da tabar ibilis ta wiwi da ya kai kilogram 2.6, adadin da ya wuce gram 500 din da ake zartar da hukuncin kisa a kansa a kasar  ta  Singapore.

A bisa dokokin kasar Singapore din dai duk mutumin da aka kama da fiye da gram 500 na wiwi za a zartar  masa da hukuncin kisa..

Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama dai sun ta kiran mahukuntan Singapore da kada su zartar da hukuncin kisa a kan mutanen amma dai suka ki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like