Zazzabin Lassa Ya Kashe Wata Mace Yayin Da Ake Cigaba Da Sa’ido Akan Mutane 65 A Jihar Anambra  An tabbatar da mutuwar wata mata mace daya sanadiyar zazzabin Lassa yayin da ake sa’ido akan wasu mutane 65 ko zasu nuna alamun kamuwa da cutar.

Darakta mai lura da harkokin Lafiya da suka shafi jama’a,  a ma’aikatar lafiya ta jihar Anambra, Dakta Emmanuel Okafor ya bayyana haka.

Okafor ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai jiya a garin Awka, yace matar da ta mutu daliba ce a wata makarantar koyon aikin jiya mai zaman kanta a karamar hukumar Idemili ta arewa.

An kwantar da matar a asibitin koyarwa na Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu dake Awka, a ranar 11 ga watan Yuni. 

 Yace tuni aka garzaya da matar  zuwa babban asibiti na Irua dake jihar Edo, domin ayi mata gwaje-gwaje inda anan Allah ya karbi ranta ranar 14 ga watan Yuni. 

” Tana karatu a wata makarantar koyon aikin jiya mai zaman kanta  dake Nkpor,ta fara zubar da jini ta dadashi, a asibitin koyarwa ta cigaba da  zubar da jinin ta hanci da kuma matucinta, an tabbatar tana dauke da Lassa a Irua. 

“Tun da muka tabbatar tana da Lassa muka shiga bibiyar mutanen da tayi mu’amala dasu ya zuwa yanzu mun gano mutane 65, mutum biyu sun nuna alamun zazzabi kuma tuni muka dauki jininsu muka aika dashi Irua,”yace. 

Darakatan yace ana cigaba da bibiyar ragowar mutanen, kana ya shawarci mazauna jihar kan abinda yakamata suyi wajen hana cutar yaduwa. 

You may also like