Ziyarar Birnin Tanhiya, Garin Da Ba A Sallar Jumma’a


Abu-Hidaya-na-biyu-daga-hagu-yake-buga-bandiri-300x277 (1)

A duk watan Maris mutanen Tanhiya na jamhuriyar Nijar suna gabatar da wani biki da ake kira Kirsali, wato Sallar Manoma) bikin a daji ake gabatar da shi ana daukar tazara sosai da gari a je a kafa tantina don mahalarta taron ana gabatar da wannan biki tsawon kwanaki uku, kuma a wannan karo taron tagomashi biyu ya samu, domin a taron aka nada sabon sarkin garin na Tanhiya, kuma suna gayyatar mutane daga sassa daban daban na duniya.

Mu ma kamar kowa mun samu gayyata zuwa wannan biki tare da abokin aiki Abubakar AbdurRahman Dodo na kamfanin ‘Media Trust.’

Mun bar garin garin Kano da misalin 11 zuwa garin Daura. Da yake ranar ta juma’a ce a garin Fago muka yi sallar juma’a. Karfe biyu daidai muka shiga garin Daura wata sa’a da muka samu shi ne muna zuwa muka samu motar Zinder, sa’a kan sa’a mun soma tafiya sai direban motar yake tambayarmu daga Zinder ina zamu?

Muka ce masa Tanout muka nufa ashe shi ma can za shi don haka muka hada masa kudin motar zuwa Tanout.

Tafiya ta soma tafiya cikin yan sa’o’i kadan muka yada zango a Zinder aka aje fasinjoji, muka yi sallah muka ci abinci bayan mun dan huta kadan, sai ‘yan kamasho suka karawa motarmu fasinja muka nausa hari sai Tanout.

Daga Zinder zuwa Tanout tafiyar Sa’a uku ce, amma da yake hanya ba kyau sai da muka shafe awa hudu a gajiye likis muka isa garin ba mu zame ko ina ba sai gidan Firife na Tanout. Sojoji ne suka mana iso zuwa cikin gidan, bayan mun gabatar da kanmu a wurin Firife sai yake gaya mana ai tuni sako ya zo masa a kan zuwanmu, gaskiya mun samu kyakkyawar tarba a wurin Firefe bayan gajeriyar hira kai tsaye masauki aka kai mu.

Da safe bayan mun kintsa mun yi karin kumallo sai mota ta zo ta dauke mu zuwa ofishin Firife wajen da za a taru zuwa Tanhiya a nan na ga Manyan mutane Mahukunta daga sassa daban-daban na kasar Nijar, bayan mun gaisa da Firefe Tanout sai ya shiga gabatar da mu a wurin manyan baki.

Cikin fara’a da barkwanci muka gaisa da kowa har suna tsokanarmu da cewa mun zo kenan basu barinmu mu koma Nijeriya, daga nan sai Firifen Tanout ya jagoranci walimar da aka shiryawa manyan baki nan muka sake cika cikinmu, bayan an gama walima sai aka shirya sansanin tafiya mu dama tuni Gwamna ya hada mu da abokanan aiki na Gidan Rediyo da Talabijin din kasar shiyyar Zinder Mai suna ORTN.

To da yake ni ina tare da kyamarar daukar hoton Bidiyo sai na ki shiga motar da gwamna ya sani na shiga landirobar sojoji da nufin idan an soma tafiya na dinga daukar masu tafiya.

Da sojojin motar suka gan ni a motarsu sai suka nuna rashin yardarsu a kan zamana a motar amma ni sam na ki nace a nan zan zauna ban san lokacin da direban motar ya je ya gayawa gwamna ba sai kawai ganin gwamna na yi ya zo ya ce na koma motarmu haka nan na sauko na koma motarmu ina ‘yan kunkuni.

Cikin ‘yan mintuna mu ka soma tafiya na dauka tafiyar irin ta Kano zuwa Zinder ce ashe ba ita ba ce, daji muka nausa tafiya muke muna dada shiga cikin Sahara kamar ba za mu daina ba ga hanyar ba kwalta shahara ce kawai ga gwajab-gwajab, ashe ba karamin sa’a ba na samu da na dawo motarmu dan har wuntsilawa muke idan muka shiga wani kwarin, duk karsashina ya ragu tun ina cewa an kusa ana da saura har na gaji na dena tambaya.

Ina ji ma’aikatan gidan talabijin suna magana da Zabarmanci suna dariya da alamu da ni suke, sun ga na gaji na yi lagwaf. Ban san lokacin da na yi bacci ba, sai kawai ji na yi ana cewa, ‘Malam tashi an zo!’ Dandazon Rakuma na hango can nesa damu bayan mun karasa gurin taron baka jin komai sai ihun Buzaye.

Mun je har an soma gabatar da taron amma muna zuwa sai aka dakatar da taron aka dauke mu tare da manyan baki zuwa masaukai.

Kafin nan dama kowa an tanadar masa masaukinsa domin ko wani daki da sunan mutanen da za a sa wadanda aka gayyata.

 

  • Allah Daya Gari Bamban

Ban taba tsammanin zan ga dan adam a wannan tsibirin ba bayan doguwar tafiya da muka sha a baya daji ne iya ganinka kuma Sahara ce zalla.  Sai gashi mun cimma gari ciki har da mutane. Wani abin mamaki shi ne yanayin dakunan mutanen garin ba irin na Arewancin Nijar ba ne, dakunan irin na bukkokin nan ne wanda kofofin kanana ne sosai sai ka sunkuya da kyau sannan za ka shiga ciki wannan su ake kira dakunan Bugaje.

Bayan mun huta mun ci abinci mun yi sallar Azahar da La’asar sai kuma muka dunguma zuwa wajen bikin, a ranar na ga asalin Buzaye irin wadanda ake kira Buzaye duk su ne a wajen suna ta wasannin al’ada kala-kala bayan an gama wasanni sai kuma aka shiga gabatar da manyan baki tare da makasudin taron.

Da yake Sallar Lasar Gishiri ce sai shugaban harkar noma ya mike ya gabatar da sabbin kayan noma da gwamnatin kasar ta samar da kuma magungunan dabbobi wanda za a rika basu kyauta don inganta kiwonsu.

Daga nan kuma sai gwamnan Zinder ya mike ya yi jawabi kan zaman lafiya a kasar Nijar. Sannan aka shiga wakoki daga bakin mawaka wadanda aka gayyata irinsu Duda mai waka da Aliyu sai kuma mawakan garin Tanhiya da na Agadez duka sun nishadantar da baki a wajen taron.

Daga nan kuma kai tsaye sai aka fara kiran Buzaye mahaya dawakai da rakuma na gari-gari domin su gaida manyan baki tare da nuna kwarewarsu a kan rakuma da dawakansu. Garuruwan da suka samu halartar taron akwai; Agadez, Taskir, Goure da Tanhiya.

Daga nan sai aka shiga babban al’amari wato yi wa sabon sarkin Tanhiya nadi a matsayin Sarki Mai Gafaka ana gama nadawa Sarki rawani sai na ji Buzayen nan sun gauraye wajen da ihu alamun mubaya’a ga sabon Sarkin nasu Ahmad Aghali Ibbah.

Daga nan sai Magajin Gari ya yi kira ga sabon Sarkin a kan ya rike ‘yan kasar sa da amana kamar yadda suka san shi dama mai amana ne. An kira Firifen Tanout ya yi jawabi da godiya ga mutanen garin Tanhiya dangane da yadda suke zaune lafiya da junansu duk da cewa suna da bambancin jinsi.

Daga nan sai Sarki Ahmad Aghali Ibbah ya amshi abin magana ya yi jawabin godiya ga mahalarta taro sannan ya yi kira ga gwamnatin kasar Nijar a kan ta samarwa da yankin na su sabis na wayar salula saboda su dinga gaisawa da dangin su na nesa kasancewar nan inda suke daji ne da kuma tsaro a yankin nasu don maganin barayi masu satar musu Bisashe (Rakuma) haka nan ya yi korafi game da rashin asibiti a yankin nasu, inda yace Tanhiya babban gari ne, kuma akwai mata da yawa suna haihuwa, amma ba asibiti dan haka yana kira ga gwamnatin kasar Nijar ta gina musu asibiti a wannan yanki nasu.

Daga karshe, ya yi kyautar Rakuma ga Firife na Tanout da na Zinder bisa jajircewarsu wajen ganin taron ya yi yadda ake so. Daga nan aka buga tambari tare da jawabin godiya da nufin gobe a karasa sauran wasanni.

To ganin an yi duk abin za a yi a wannan rana sai mafi yawa daga cikin manyan bakin da suka zo kowa ya kama hanyar komawa gida ciki har da gwamnan Zinder da Sultan.

Washe gari aka ci gaba da sha’anin bukuwa dana sarauta da yake Buzayen jinsi-jinsi ne sai ya zamana shigarsu ma daban-daban ce.

 

  • Buzayen Sun Kasu Kashi Uku

Akwai makeran Buzaye akwai Jajayen Buzaye da kuma Buzaye Abzinawa wani abin al’ajabi ba sa auratayya a tsakaninsu, kowa sai dai ya auri jinsinsa.

Sannan wani karin abin mamaki a garin shi ne ba a Sallar Juma’a, dalili kuwa shi ne ba su da masallacin Juma’a, sai dai duk ranar juma’a mutanen garin su taru a fadar Sarki a yi sallar Azahar sannan a yi jawabai daga nan kowa ya koma gida.

A wannan rana aka kira mahaya Rakuma da suka zo daga gari-gari aka musu kyautar wadanda suka fi iya sarrafa Rakumi da kuma kwalliya.

Sannan aka shiga wake-wake a wannan ranar kuma mawakan da suka nishadantar sun hada da Mawaki Abdallah daga jahar Agadas da kuma wata tsohuwar Mawakiyar garin mai kidan Goge.

 

  • Na Tsallake Rijiya Da Baya

Dana ga ana ta shagali a wurin taro sai na zame na shiga gari neman ruwa da yake ruwan roba muka ta fi da shi kuma duk ya kare gashi kuma ana ta kwalla rana, duk inda na je da kyar ake ban ruwa amma sai inga ruwan bai yi min ba, na tambaya inaIMG-20160805-WA023suke samun ruwan suka nuna min wata hanya wai idan na bi ta zan samu ruwa to da yake ina tare da kyamarata sai na ji dadin hakan domin ina son in dauko inda suke samun ruwa musamman yadda na lura ana wahalar ruwa a yankin.

Na jima ina tafiya sai na fara hangen wani tarin abu nesa dani, ina matsawa kusa sai na lura ashe tarin Rakuma ne da dabbobin Buzayen suka kewaye wani abu, da kyar na isa wajen duk na galabaita kishirwa ta kama ni da yawa da isata na tarar da Buzaye ne rakwacam su da matansu da tarin dabbobi ko wani buzu fuska rufe kuma rataye da takobi.

Aradu sai da na gwammace ban je gurin ba, domin wata rijiya na gani ban taba ganin irin ta ba, sai ko a tarihi, katti hudu ne a bakin rijiyar suke dauko gugan, kuma shanu ake daurawa wata doguwar igiya a yi ta duka sai sun yi tafiya mai nisa sannan gugan zai zo bakin rijiya su kuma Buzayen sai su kama da kyar su fito da shi su zuba a wani katon duro da suka tanada.

Yanayin kallon da na ga suna min sai nasha jinin jikina na ce musu ni bakon sarki ne daga Nijeriya ruwa na zo sha, suka nuna min wajen da zan sha ruwan ina zuwa na tarar da mutane da Jakuna da Rakuma, har da tinkiyoyi gami shanu duk suna shan ruwa a wata kwatanniya mamaki ya kama ni, na ce a raina yanzu wadannan mutanen ba sa tsoron cuta suke shan ruwa tare da dabbobi?

Ina tsaye sai na ji wata mata ta min magana cikin gurbatacciyar Hausa “Ke namiji jo ki sha ruwan,” gaba na ya fadi lokacin dana ga ruwan da ta miko min, yanzu wannan ruwan zan sha? Dana je wajen da ta debo ruwan na ga yadda ruwan yake sai da hantar cikina ta kada, ruwan ya zama kamar ruwan kwatami ga ledoji nan da yayi birjik a ciki, duk da kishirwar da nake ji sai na ji bazan iya shan ruwan nan ba.

Na ce mata, ‘Na gode,’ na juyo zan dawo masauki haba sai na ji kamar ba zan iya taku goma ba zan fadi domin na sha rana da tafiya cikin sahara kun san ba kamar tafiya hanya cikakka ba, ga kuma kishirwa, dole na juyo wajen matar nan na ce ta ban ruwan na sha, haka na rufe idununa na sanya rigata ta zama matatar hakukuwan ciki, na sha ruwan nan sosai domin kishirwa ta ci karfina, bayan na gama sha sai na dauko kudi na ba matar nan. Haba wa! Ashe hakan da na yi laifi ne, ba a ba matansu kudi. Yin hakan ga wani bare kamar kana son mace ne. Sai na ji wani Buzu ya kurma ihu, ‘Ayyyiii!’

“Karya kake namiji ke ba shi kudin shi,” yadda na ga Buzayen sun nufo ni sai na fara salati tsammani na tawa ta kare, suna zuwa sai suka amshi kudin da na ba ta, suka dawo min da shi.  Wani dattijo daga cikinsu ya ce, “Ko kai bakon Sarki ne?” Na ce ‘E.’

Sai ya ce, “To ko Bisashe (Rakuma) nawa ka kawo nan suka sha ruwa bakka biyan ko sisi je ka abinka,” ni dai cikin tsoro na baro su.

Wata sabuwa, in ji ‘yan caca! Ina dawowa gari sai tarar da abokin tafiyata wato Abubakar Dodo ya bi Firifen Tanout sun tafi IMG-20160805-WA019kuma dama tawagarmu ce kawai ta rage ba ta tafi ba, nan fa idona ya raina fata yanzu ya zan yi? Gashi kuma na ji sun ce ko a Rakumi kafin mutum ya cimma babban gari sai ya kwana hudu a hanya.

Ina cikin zulumi sai na hangi mataimakin Firife na Tanout can tare da Sarki, haba ai tuni raina ya yi fari, na je na tarbe shi muka gaisa ya yi mamaki da ya gan ni ya ce, “Me kake a nan ba ka tafi ba?

Na ce masa tafiya aka yi aka bar ni, sai ya ce to na yi hakuri na dan jira shi ya gama ganawa da Sarki shi yanzu zai tafi, na ce masa, ‘To,’ na koma gefe na zauna muka shiga hira ni da wani abokina Buzu, yana ta ba ni labari garin da al’adunsu a nan na gane ashe idan suka ce Fulani (Dosawa) Bararoji suke nufi, na ce masa wai zaman me suke a wannan daji ga gari can sun zo nan sun zauna?

Sai ya ce da ni ai su nan zaman Rakumansu suke, yanzu da zasu tatsi nono a jikin Rakumi suka ga ba kamar yadda suka saba da tatsa ba ko kuma suka ga Rakumansu suna ramewa to a ranar za su bar dajin su yi gaba, ya ce min a nan dana ke ganinsu akwai mai Rakumi Dari Uku akwai mai Dari Biyu, dana masa maganar abinci sai ya ce min in dai da hatsi da kuma nonon Rakuma su ai lafiya lau ne.

Muna tsaka da hira sai ga Mataimakin gwamnan Tanout ya fito muka yi sallama da Sarki da abokina na shiga mota koma Tanout.

Ina zuwa Tanout na hadu da abokin tafiyata muka gaisa, ya ce, ai sun neme ni, ba su ganni ba, shi ne Firife ya ce su tafi za a taho da ni.

Daga nan muka je muka yi sallama da Firife tare da godiya muka shirya kayanmu hari sai gida Nijeriya.

Taron dai ya samu halartar mutane da dama daga kasashen ketare musamman ‘yan yawon bude ido kuma an yi lafiya an gama lafiya.

Mun dawo gida iso gida Nijeriya lafiya, ranar litinin da misalin karfe daya na rana.

 

 

 

 

 

cc: Abu Hidaya Marubuci ne kuma dan jarida mai zaman kansa. Ya aiko mana wannan ne daga Kano. 08065025820.

You may also like