Zuwan Rasha wasannin Rio na tangal-tangal


 

Hukumar da ke yaki da shan kwayoyi a wasanni ta duniya WADA ta gudanar da wani bincike kan harkokin wasannin a kasar ta Rasha inda ta nemi a dakatar da kasar.

 

Kwamitin kasa da kasa da ke shirya wasannin Olympic ya dakatar da ministan wasanni na kasar Rasha Vitaly Mutko daga wasannin da za a yi a birnin Rion na Brazil, sannan ya janye da goyon bayan da yake ba wa shirin wasannin kasa da kasa a Rasha saboda badakalar amfani da kwayoyi da ke kara kuzari ga ‘yan wasa, sai dai kwamitin bai kai ga tsaida kasar baki daya ba daga shiga wasannin na Rio har sai sakamakon kotu ya bayyana a ranar Alhamis.

Wasannin dai na birnin Rio za a farasu ne a ranar biyar ga watan Agusta, a ranar Talata kwamitin na IOC ya yi wani zama na gaggawa kan abin da shugaban wasannin na Olympic Thomas Bach ya bayyana da ” abu mai sosa rai da kokarin zubar da kima ta wasannin na Olympic daga mahukuntan na Rasha.

Hukumar da ke yaki da shan kwayoyi da kan kara kuzari a lokutan wasanni ta duniya WADA wacce ta gudanar da wani bincike mai zaman kansa kan harkokin wasannin a kasar ta Rasha ta bukaci a tsaida kasar ta Rasha daga wasannin na Rio.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like